Kotu a Makkah ta wanke limami daga tuhumar cin zarafin mata

Wata kotu a yankin Makkah a ƙasar Saudiyya ta wanke wani limamin masallaci daga tuhumar da ake yi masa ta cin zarafin mata masu aikin gidansa.

Kotun ta yi watsi da ƙarar bisa hujjar cewa waɗanda suka shiga da ƙarar sun gaza gabatar da ƙwararan hujjojin da za su tabbatar da zarginsu.

Daga ƙarshe kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin korar ƙarar, kamar yadda jaridar intanet ta Saudi Gazette ta ruwaito.

Mai shigar da ƙara na gwamnati ne ya miƙa ƙarar bayan da ya gudanar da bincike kan ƙorafin cin zarafin da aka shigar a kan limamin masallacin, wanda ɗan asalin Saudiyyan ne.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wata kotu a Saudiyya a karon farko ta bayar da izinin bayyana sunan wani mutum da aka kama a laifin cin zarafin mata da kuma kunyata shi a bainar jama’a, kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.

Wata kotun hukunta masu manyan laifuka a Madina ce ta kama Yasser al-Arawi da laifin cin zarafin mata ta hanyar amfani da kalaman batsa.

An yanke masa hukuncin ɗaurin wata takwas a gidan yari da tarar dala 1,330.