Buhari Bai Hana Ni Yin Takara Ba – Tinubu
“Ban sanar da ‘yan Najeriya ba tukuna domin ina ci gaba da tuntubar mutane domin neman shawara. In ji Tinubu.
Tsohon gwamnan Jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce shugaba Muhammadu Buhari, bai hana shi tsaya wa takarar shugaban kasa ba da ya fada masa burinsa na kokarin zama wanda zai gaje shi a 2023.
A ranar Litinin Tinubu ya fadawa manema labarai hakan jim kadan bayan wata ganawa da ya yi da Buhari a fadarsa da ke Abuja.
“Cikakken dan dimokradiyya ne (wato Buhari) bai ce min na dakata ba, bai kuma ce min kada na bi burina ba.” Tinubu ya ce.
A cewar tsohon gwamnan na Legas, batun neman shugabancin Najeriya abu ne da ya jima yana burin ganin ya cimma a rayuwarsa.
Ko da yake, a cewar Tinubu har yanzu bai fito fili ya fadawa ‘yan Najeriya wannan muradi nasa ba, amma ya ce a kasa kunne, nan ba da jimawa ba za a ji daga gare shi.
“Ban sanar da ‘yan Najeriya ba tukuna domin ina ci gaba da tuntubar mutane domin neman shawara.”
“Ina da kwarin gwiwa, hange, da kwarewar iya mulki da zan dora akan turakun da shugaban kasa ya kafa don samarwa Najeriya makoma ta gari, na taba yi a jihar Legas.” Tinubu ya kara da cewa.
Da ma dai an jima ana rade-radin Tinubu mai shekaru 69 zai nemi takarar shugaban kasar, duba da yadda wasu kungiyoyi da fitattun mutane suke kokarin tallata shi a idon ‘yan Najeriya.