APC ta maida wa Shehu Sani martani

Jam’iyyar APC ta maida wa sanata Shehu Sani martani inda ta ce shugabancin jihar Kaduna ba ta masu kashe wando bane a yanar gizo. 

Martanin wanda Tanko Wusono ya rubuta ya yi suka ga jam’iyyar PDP cewa har yanzu jam’iyyar bata daura kambu da banten iya kada APC a jihar Kaduna ba.

A hira da sanata Shehu Sani yayi da da wata gidan Radiyo wanada jaridu da dama suka wallafa, sanatan ya ce babban burin sa yanzu shine ya dare kujerar gwamnan Kaduna domin ya tsaftace jihar daga abin da yakira kazantar da gwamnatin APC ta kawo jihar.

” Bani da kudin da zan biya deliget su zabe ni amma, domin kudin da ke narka wa deliget su yi zabe ne ya jefa mu cikin halin da muke ciki a kasar nan.

” Idan talakawa suka zabe ni, da kudi ba kudi zan yi nasara.”

” Na zauna da masoyana kuma duk sun amince min in fito in yi takarar gwamnan Kaduna a 2023 kuma na amince zan fito takaran domin in wancakalar da dan lele kuma zabin gwamnan jihar da kuma shiga gidan gwamnati inda za a rantsar da Kwamared a matsayin gwamnan da zai kawo sauye-sauye, wanda zai share duk wata kazantar da suka kawo jihar da sunan ci gaba.

Sai dai kuma Jam’iyyar APC ta jihar Kaduna ta maida masa da kakkausar Martani inda Sakataren yada labarai na jam’iyyar Tanko Wusono ya ce mutanen Kaduna ba za su bari wasu marasa gaskiya su mayar da su baya ba.

” Tun a watan Mayun 2015, jam’iyyar APC ta dora jihar Kaduna a kan turbar ci gaba mai dorewa da ci gaba. Ta hanyar gyare-gyaren manufofi da dokoki da ayyuka na zahiri.

” 2023 za ta kara tabbatar da cewa jihar Kaduna ba fage ce ga wadanda ba su taba gudanar da komai ba a jihar, wadanda ba su san me ake nufi da ci gaba ba sannan kuma da wadanda suka dauka shugabantar jama’a musamman jiha irin ta Kaduna wasan kwaikwayo ne.

” Jihar Kaduna ba jiha bace ta wadanda kullum sai yin burga da kurin sun san jihar sun yi aiki a jihar amma babu wani abu da zai nuna cewa wai gwanaye a jihar, haka kuma ba jiha bace ta irin wadanda kaddara ta kaisu ga kujerar gwaman amma maimakon su maida hankali wajen inganta mutane sai suka karkata zuwa rangada kwalliya suna kokuwar neman sarauta da jijji da kai, ko ku, a jiha ta wadanda a kullum sai da su rika tsince-tsince suna kashe wandu a yanar gizo.