Hukumomi a Sudan sun toshe layukan sadarwa

Hukumomi a Sudan sun toshe layukan sadarwa a daidai lokacin da masu zanga-zanga ke taruwa a wasu biranen ƙasar domin soma zanga-zanga ta farko a bana.

Jami’an tsaron ƙasar sun sa shingaye inda suka rufe wasu hanyoyi a Khartoum babban birnin ƙasar.

Masu zanga-zangar dai na neman sojojin ƙasar su bar siyasa su miƙa mulki ga farar hula.

Wannan zanga-zangar ita ce babbar zanga-zanga ta 12 da ake gudanarwa tun daga watan Oktoban bara bayan sojoji sun yi juyin mulki ga gwamnatin Firaiminista Abdallah Hamdok.

Sai dai sojojin sun mayar da shi kan muƙaminsa bayan wata guda amma daga baya an ci gaba da zanga-zanga.

Sama da mutum 50 aka kashe tun bayan da aka soma wannan zanga-zanga.