Duniya na ci gaba da juyayin rashin Desmond Tutu
Shugabanni kasashen duniya na da da na yanzu, na ci gaba da nuna alhininsu ga iyalai da dangi da ma hukumomin Afirka ta Kudu bayan rasuwar Archbishop Desmond Tutu a ranar Lahadi.
Mutuwar Archbishop Desmond Tutu ta kada al’umma da ke ciki da wajen Afirka ta Kudu, kasancewar sa a matsayin dan gwagwarmayar da ya taka rawar gani wajen kawo karshen wariyar launi fata a kasar. A sakon ta’aziyarsa, tsohon shugaban kasar Amirka bakar fata ta farko Barack Obama, ya bayyana marigayi Tutu a matsayin wanda ya jajirce a kan tafarki mai kyau, ya kuma yi tsayin daka a gwagwarmayar neman ‘yanci da adalci a kasarsa da kuma ko’ina a fadin duniya.
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ya ce Desmond Tutu ya kasance mai fafatukar kare ‘yancin dan Adam, kana mai kokarin samar da ‘yanci da kuma daidaito.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Firaministan Birtaniya Boris Johnson, ya ce Tutu wani jigo ne a yakin da ake yi a kan wariyar launin fata da kuma gwagwarmayar samar da sabuwar Afirka ta kudu wanda ba za a manta da irin dattakunsa ba.
A nata sakon Mary Robinson da ke zama tsohuwar shugabar hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya kana tsohuwar shugabar kasar Ireland ta ce Tutu ya kasance cikin jerin mutane da ba za a taba mantawa da su ba.
Ta ce “Mutum ne mai kirkin gaske, a tsawon rayuwarsa ya kasance mai karamci ya taba rayuwar mutane da dama kuma ba za a manta da karamcinsa ba da kuma tausayinsa da kaunar juna. Ya kan yi magana kan kaunatar juna a koda yaushe.”
Tuni dai aka yi kasa-kasa da tutar kasar don nuna alhinin mutuwarsa. Yayin da yake jawabi, shugaban kasar Cyril Ramaphosa na cewa:
“Marigayin ya sani a ransa cewa nagarta za ta yi nasara kan mugunta yayin da adalci zai rinjayi rashinsa haka kuma zaman sulhu zai rinjayi daukar fansa. Kazalika wata rana za a kawo karshen mulkin wariyar launin fata kuma demokradiyya zata tabbata.”
Marigayi Tutu wanda ya kasance na hannun daman tsohon shugaban kasar, marigayi Nelson Mandela, ya sami kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekarar 1984 saboda rawar da ya taka cikin lumana wajen yin adawa da shugabancin farar fata tsiraru. Bayan shekaru goma kuma ya shugabanci kwamittin sulhu domin dinke ta’asa da kuma baraka tsakanin mutane.
Ba ga kasarsa ba kawai, marigayi Desmond Tutu ya kasance jakadan wanzar da zaman lafiya da kuma warware rikici a wasu kasashen. Ko a shekarun da suka gabata ya taka rawar gani a kawo karshen rikicin bayan zabe da ya barke a kasar Kenya, kamar yadda ‘yan kasar ke alfahari da hakan.
Ana sa ran binne tsohon dan gwagwarmayar wanda ya mutu ya na da shekaru 90 a ranar daya ga watan Janairun badi a birnin Cape Town na kasar, inda shugabanni daga sassa daban-daban za su halarta.