Mutum 8 sun mutu a harin jahar Filato

Shedun gani da ido sun tabbatar da labarin harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kan wata kasuwa da yayi sanadiyar rayukan mutum 8 a jahar Filaton Najeriya.

A yammancin ranar Lahadin da ta gabata ne, maharan suka far ma kasuwan inda suka bude wuta kan jama’a da ke tsakiyar hada-hadar kasuwanci a kauyen Pinau da ke karamar hukumar Wase a jahar Filaton Najeriya, mazauna yankin na cewa wadanda suka mutun sun haura goma sha daya amma rundunar ‘yan sanda ta bakin kakinta Ubah Ogaba, ya ce, ba su kai ga iya tantance yawan wadanda suka mutu a harin ba.

Pinau da ke karamar hukumar Wase ya jima yana fama da hare-hare da ake dangantawa dana kabilanci ko addini, kokarin shawo kan matsalar tsaron da hukumomi ke yi a yankin bai yi wani tasiri ba,  ganin cewa, hare-haren na lafawa ne inda bayan wani dan lokaci, ake samun munanan hare-hare masu tayar da hankulan jama’ar jahar. Najeriya na daya daga cikin kasashen Afrika da yanzu ke fuskantar tarin matsalolin tsaro musanman a yankin arewacin kasar.