ECOWAS : Taro kan rikicin Mali da Guinea Conakry

Shugabannin kasashen yammacin Afirka za su dukufa don lalubo mataki na gaba kan sojojin da suka kifar da gwmnati a Mali, bayan kin mutunta kudrin ECOWAS na shirya zabe don mika mulki ga farar hula.

Tun bayan juyin mulkin da soja suka yi a Mali har sau biyu, mahukunta na Mali suka shiga takon saka da kungiyar ECOWAS game da batun shirya zaben da sake ba da mulki a hannun wata zabbabiyar gwamnati, lamarin da ya janyowa kasar jerin takunkumai na karayar tattalin arziki da ma na tafiye-tafiye ga manyan jami’an gwamnatin.

Ko ba ya ga Mali shugabannin kasashen ECOWAS za su kuma duba halin da ake ciki a kasar Guinea Conakry, musamman ma batun shirya zabe da sakin tsohon shugaban kasar Alpha Conde da soja suka hambarar. Batun annobar corona sabon nau’i ma da takunkumin hana tafiye-tafiye da wasu manyan kasashe suka gindaya wa wasu kasashen Afirka na daga cikin batutuwan da za su tattauna.