Biden ya dawo da dokar hana baƙi shiga Amurka
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama na Amurka sun soki sake dawo da wata manufa ta gwamnatin Trump da ta bukaci masu neman mafaka su jira a Mexico har sai an kammala bincike kan buƙatarsu.
Hukumar kula da shige da fice ta Amurka ta ce rana ce marar dadi ga Amurka da dokar ƙasa.
Shugaban Amurka Joe Biden da ya dakatar da manufar, bayan ya kira ta da “rashin imani”, amma kotu ta umurci a dawo da ita.
A karkashin manufar, an tilastawa dubban bakin haure zama cikin yanayi mai hadari a kan iyakar Mexico.
Sai dai ‘yan jam’iyyar Republican sun yi maraba da matakin a matsayin wata hanya ta mayar da da zaman lafiya a yankunan kan iyaka.
Gwamnatin Mista Biden ta ci gaba da yin wasu manyan manufofin kan iyaka na mulkin Trump