Matafiya Sun Shiga Tsaka Mai Wuya Sakamakon Tsadar Tikitin Jirgin Kasa na Kaduna Zuwa Abuja

Fasinjoji a tashar jiragen kasa a Kaduna na ci gaba da kokawa kan yadda wasu mutane da ake zargin ba ma’aikatan hukumar NRC ne ba ke saran tikiti tare da saidawa da tsada kama daga naira dubu bakwai. 

Wannan lamarin dai ya tilasta wa fasinjoji suka rika sayen tikitin a kan farashin dubu bakawi wanda ya yi tsada ga talakawa a hannun ’yan kasuwar bayan-fage da ba a iya tantance ko su wane ne ba, kamar yadda wani matafiyi, Suleiman Abdulrazak ya shaida.

Abdulrazak ya shaida cewa a ranar juma’ar da ta gaba ne ya lura da cewa shafin sayar da tikitin yanar gizon hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya wato NRC ya daina aiki, lamarin da ya sa shi da wasu fasinjoji suka koma sayen tikitin a tashar jirgin kasa.

“Ana zargin wannan lamari ya ba wasu ma’aikatan hukumar ta NRC damar hada baki da ’yan cuwa-cuwa wadanda suka sari tikitin suna sayarwa da tsada don samun kazamar riba ba tare da jin tausayin talakawa ba.”

Halin tsaron da ake ciki kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ya tilasta wa matafiya yin tururruwa zuwa tashar jirgin kasar domin tsira da ransu.

Fasinjojin na kokarin kauce wa masu garkuwa da mutane ne don neman kudin fansa a hanyar Kaduna zuwa Abuja, muddun suka bi hanyar mota.

Tsohon mai bai wa gwamnatin jihar Kaduna shawara a kan harkokin addini, Malam Halliru Abdullahi Maraya, ya ce yanayin tsaro a Arewacin Najeriya ya kai ga mutum ya yi shahada idan zai bar gida don rashin tsaron da ake ciki a cikin gari da ma kan hanyoyi ya wuce inda ake tunani.

Maraya ya kuma yi kira ga gwamnatin kasar ta sake nazarin matakan shawo kan matsalolin tsaro da ake ciki a fadin kasar musamman ma Arewacin Najeriya.