Barayin daji a Zamfara sun kona gari da sace mutane

Rahotanni daga Najeriya, na cewa mutane sun tsere daga ƙauyen ‘Yan Ɓuki cikin ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, bayan wani harin ‘yan fashin daji da ya yi sanadin hallaka mutum bakwai. 

Wani mazaunin ƙauyen da shi ma ya tsere zuwa Gusau ya ce da misalin karfe 12 na rana ne maharan su ka shigo garin, tare da bude wuta, sun kuma shiga gidaje su na fito da mata da kananan yara da maza har da tsofaffi sama da 50, sukai cikin daji da su, sannan sun ƙone musu dukiyar da ba a san adadinta ba.

Mutumin ya ce su ma Allah ne ya kubutar da su, suka samu tserewa tare da shiga motar da ta kai su birnin Gusau, ”bayan mutanen da suka tafi dasu, sun kuma kashe mutum 7, ciki har da dan uwana uwa daya uba daya mai suna Abdullahi har cikin daki su ka shiga su ka fito da shi, ya na turjewa amma haka suka harbe shi a baya da kuma makoshinsa,” in ji mutumin da bai so a bayyana sunansa ba.

Sai dai kawo yanzu ‘Yan sanda ba su tabbatar da wannan harin ba.