An yanke wa wasu fararen fata hukuncin kisa kan kashe wani bakar fata a Amurka
Shugaba Biden na Amurka ya yi maraba da hukuncin da aka yankewa wasu farar-fata uku wanda suka kashe wani bakar-fata da ke motsa jiki, Ahmaud Arbery, a lokacin yake atisaye a cikin unguwa a jihar Georgia.
Shugaban ya ce kisan, abu ne na kaduwa da ke tunasar da jan aikin da ke gaban Amurka wajen yaki da wariya.
Linda Dunikowski, babbar mai gabatar da karar ta ce gaskiya tayi halinta, kuma wannan shi ne burinmu na ganin anyi adalci.
Wadanda aka yankewa hukuncin, George McMichael da Travis McMicheal da William Bryan, sun yi ikiarin cewa sun aikata hakan ne domin kare kansu, suna cewa Mr Arbery ya yi kama da barawo.
Yanzu haka suna fuskantar hukuncin daurin rai da rai kan kisa.