E-Naira: ‘Yan damfara sun tilasta wa CBN sauke manhajar daga Play Store da App Store

Shagunan sayar da manhajojin salula sun sauke manhajar kuɗin intanet na e-Naira daga shafukansu kwana uku bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da ita. 

A safiyar Alhamis ne aka lura babu manhajar ta e-Naira a shagunan Play Store (masu Android) da kuma App Store (masu Apple). 

Sai dai wasu da suka sauke manhajar tun farko sun ce tana aiki a wayoyinsu zuwa lokacin haɗa wannan rahoton. 

Lamarin na zuwa ne daidai lokacin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ankarar da ‘yan Najeriya game da ayyukan wasu “miyagu” da ke yunkurin cutar mutane da sunan e-Naira.

Mutanen a cewar CBN, sun buɗe wasu shafukan sada zumunta da sunan babban bankin inda suke yada cewa yana raba kudin e-Naira har biliyan 50. 

A ranar Litinin da ta gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari tare da Mataimakinsa Yemi Osinbajo suka kaddamar da kudin na e-Naira a Abuja, babban birnin kasar. 

CBN ya ce ya samar da kudin ne domin bai wa kowane rukuni na ‘yan Najeriya damar gudanar da harkokin kudinsu cikin sauki bayan ya haramta amfani da sauran kudaden intanet na cryptocurrency.

Babban bankin na Najeriya ya fada cikin wata sanarwa ranar Laraba cewa “miyagun” na kokarin cutar ‘yan Najeriya ne wadanda ba su ji ba su gani ba. 

“CBN ya lura da ayyukan wasu miyagu da kuma wani shafin Twitter mai suna @enaira_cbdc da aka ce na CBN ne,” a cewar sanarwar. 

“Shafin na bogi da kuma mutanen suna ta yada sakonnin da suka shafi e-Naira da zummar jawo hankalin ‘yan Najeriya da cewa CBN na raba e-Naira biliyan 50. 

‘Wadannan miyagun sun dage sai sun zalunci mutane ta hanyar maƙala wani adireshi a jikin saƙonnin nasu suna rokon mutane su shiga domin samun kasonsu a biliyan 50 din.”

Tun farko CBN ya ce an samar da e-Naira ne ta hanyar fasahar da ake kira Blockchain Technology da zummar ba ta tsaro ta yadda ba za a iya yin jabunta ba.