Ana gwabza fada tsakanin dakarun Ethiopia da ‘yan tawaye

A kasar Ethiopia, rahotanni na cewa ana ci gaba da gwabza fada a kusa da biranen Dessie da Kombolcha da ke jihar Amhara tsakanin dakarun ‘yan tawayen Tigray da na gwamnatin kasar da kawayensu.

Dessie gari ne mai dauke da dubban ‘yan gudun hijira da suka tsere daga gidajensu a yayin da yaki ya yi kamari zuwa makwabtan da ke kudancin Tigray.

A gefe guda, Kombolcha yankin ne mai dauke da masana’antu, kuma a nan ne babban filin jirgin saman yankin yake.

Rahotanni sun ce an sake yin luguden wuta ta sama a kan babban birnin Tigray wato Mekelle.

Ofishin sadarwa na gwamnati ya ce burinsu shi ne su hari manasa’antar Mesfin Engineering, wadda a makon jiya aka kai mata hari ta sama.

Dakarun ‘yan tawaye ba su ce uffan ba game da ikirarin kai hari kan wuraren sai dai wani babban jami’insu Getachew Reda ya wallafa sakon Tuwita da ke tabbatar da kai hare-hare ta sama kan birnin, yana mai karawa da cewa “sashenmu na kare hari daga sama” yana “mayar da martani kan jiragen makiya”.