Rahoton sakamakon binciken fyade a Kongo
Wani rahoto da aka fitar na nuni da cewar, jami’an agaji sun ci zarafin mata da maza sama da 80 ta hanyar lalata da fyade a lokacin barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Kongo.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana razanarsa game da wannan rahoto na sakamakon binciken da kwamitin da hukumarsa ta kafa.
Daya daga cikin wadanda abin ya rutsa da su wadda ke aiki a cibiyar kula da cutar Ebola, ta bayyana irin wahalar da ta sha a lokacin:
“Ina son adalci! Domin sun ci zarafinmu. Sun saka mu cikin wani hali da ba zamu iya mantawa ba. Sun tilasta yin jima’i da mu kafin su bamu aiki. Ina son a yi mana adalci! Wajibi ne a yanke musu hukunci daidai da laifin da suka aikata”.