Jami’ar soji ta zargi kasashe makwabta da ta’azzara matsalolin tsaron Najeriya
Wata babbar jami’ar sojin ruwan Najeriya ta yi zargin cewa akasarin haramtattun makaman da ake satar shiga da su kasar na da alaka da jami’an tsaron kasashe makwabta.
Rahotanni sun ambato Kwamado Jamila Abubakar, na yin wannan zargi ne lokacin da ta wakilci Babban Kwamandan sojojin ruwan kasar, Awwal Gambo, yayin wani zaman sauraron jin ra’ayoyin jama’a da kwamitin majalisar kan harkokin tsaron kasa da tattara bayanan sirri ya gudanar.
Ta dai ce makaman da kasashen da suka ci gaba ke bayarwa gudunmawa ga kasashe makwabtan Njeriya su ne ke ta’azzara matsalolin tsaro a kasar.
Shugaban kwamitin harkokin tattara bayanan sirri a majalisar wakilai na Najeriya Sha’aban Ibrahim Sharada ya shaidawa BBC cewa zargin jami’ar bai zo musu da mamaki ba ganin yanayin da tsaron kasar ke ciki.
Sannan ya ce an karbi wannan bahasi kuma za a nazarci da binciker gaskiyar batutuwan da ta gabatar da zarge-zargenta a kai.
Daga Jaridar : BBC