An yi nasarar murkushe juyin mulkin Sudan
Jama’a sun ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum a birnin Khartoum duk da rahotannin yunkurin juyin mulkin kasar a yau Talata.
Wani yunkurin juyin mulki a Sudan ya yi rashin nasara a sanyin safiyar yau Talata kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka rawaito ba tare da ambatar wadanda suka kitsa juyin mulkin ba.TALLA
Sai dai wasu majiyoyin soji da na gwamnati sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, wani gungun dakarun soji ne ya yi yunkurin kifar da gwamnatin Sudan, amma tuni aka ci galabar sa.
Wannan na zuwa ne a dadai lokacin da kasar ke fuskantar kalubale dangane da shirin mika mulki tun bayan kifar da gwamnatin Omar al-Bashir a shekara ta 2019.
Rahotanni na cewa, yanzu haka jami’an tsaro sun rufe babban gadar da ratsa Nile ta kuma sada babban birnin Khartoum da Omdurman.
Mutane dai na ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum, inda ababwan hawa ke ci gaba da zirga-zirga cikin lumana a tsakiyar birnin Khartoum da kuma harabar ginin shalkwatan sojojin kasar, inda aka kwashe watanni ana gudanar da zanga-zangar da ta yi sanadiyar kifar da gwamnatin al-Bashir shekaru biyu da suka gabata.
Gwamnatin rikon kwaryar Sudan ta yanzu, ta kunshi sojoji da fararen hula, yayin da alhakin maido da mulki hannun farar hula ya rataya akan gwamnatin ta yanzu.