“A zahiri mun dogara ne da wata hukuma da ba mu da ikon ba ta umarni kuma wannan ne ya sa za ka ga jihohi da dama sun duƙufa wurin kafa hukumomin tsaro” : Gwamna Fayemi.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya bayyana cewa halin da ake ciki musamman ta fuskar tsaro a Najeriya abar damuwa ce ga ƴan ƙasar baki ɗaya.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wata hira da BBC inda ya ce wannan matsalar tsaron da ake fama da ita su kansu gwamnoni tana mayar musu da hannun agogo baya ta ɓangaren ayyukan da suke yi wa al’umma.

Ya ce sau da dama ayyukan da aka tsara za a yi kan wargaje sakamakon hare-haren da ake kaiwa. Gwamnan ya ce suna ɗaukar matakai daban-daban wurin magance matsalar tsaro ta hanyar haɗa gwiwa da gwamnatin tarayya da al’ummomi 

Gwamnan ya bayyana cewa suna iya bakin kokarinsu, amma akwai iyakar da ba su da ikon ketarawa, sakamakon ba su da iko da jami’an tsaron tarayya duk kuwa da ana kiran gwamnoni da manyan jami’an tsaron jihohinsu.

“A zahiri mun dogara ne da wata hukuma da ba mu da ikon ba ta umarni kuma wannan ne ya sa za ka ga jihohi da dama sun duƙufa wurin kafa hukumomin tsaro da za su agaza wa gwamnatin tarayya kamar yadda ake da Amotekun da Ebube a shiyyar kudu maso yamma da kuma ƴan ƙato da gora a shiyyar arewa maso gabas,” in ji gwamna Fayemi.

A cewar gwamnan, matuƙar ƴan bindiga na ci gaba da kai wa ƴan Najeriya hari da sauran aika-aika, wannan na nuna cewa da sauran aiki, har sai lokacin da aka daƙile miyagun laifuka a ƙasarmu da jihohinmu.

Dangane da wannan ƙalubalen na tsaron da ake fuskanta a Najeriya, BBC ta tambayi Gwamna Fayemi ko yana ganin jam’iyyarsu ta APC za ta kai labari a zaɓen 2023, sai dai a cewarsa;

“Ba zan ce mun cika wa al’umma duka alƙawuran da muka ɗauka ba, har yanzu da sauran aiki, amma duk ɗan Najeriya mai adalci yana iya ganin abin da ke faruwa a ɗaya ɓangaren, abokan hamayyarmu sun wargaje, sai sauya sheƙa suke yi zuwa jam’iyyarmu”, in ji Gwamna Fayemi.

Sai dai jama’a na sukar gwamnonin jihohi da gazawa wurin samar da tsaro sakamakon yadda ake ganin sun zuba wa gwamnatin tarayya ido duk kuwa da maƙudan kuɗaɗen da gwamnonin ke samu da sunan tsaro wanda aka fi sani da security votes.

Matsalar tsaro dai na daga cikin manyan matsalolin da suka addabi Najeriya musamman arewacin ƙasar. Jihohin da ke arewa maso yammacin ƙasar na fama da ƴan bindiga da ɓarayin shanu da masu garkuwa da mutane domin karɓar fansa, inda a baya-bayan nan ma wata sabuwar matsala ta ƙara kunno kai ta satar ɗalibai.

A arewa maso gabashin ƙasar matsalar ƴan Boko Haram ce ke addabar yankin duk da jami’an tsaro na ikirarin cewa sun karya lagon su.

Haka ma a arewacin Najeriya musamman jihohin Zamfara da Katsina jami’an tsaron na ikirarin samun nasara kan ƴan bindiga inda suka ce sun kashe da dama daga cikin su da kuma tarwatsa daba-daba da ke cikin dazuka.

Ko a makon da ya gabata sai da gwamnatin Najeriyar ta bayar da umarni ga kamfanonin sadarwa su katse layukan waya domin ba jami’an tsaro damar gudanar da ayyukan tabbatar da tsaro.