Ce-ce-ku-ce tsakanin jihohi Najeriya da gwamnatin tarayya akan haraji

Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce tsakanin gwamnatocin jihohin Najeriya da gwamnatin Tarayya kan tsarin karɓar kuɗaɗen haraji kan kayayyakin more rayuwa a faɗin kasar.

Wannan ya biyo bayan bukatar da wasu jihohin kudancin Najeriya ciki har da Legas suka bayyana na a ba su damar karɓar kuɗaɗen haraji a matakin jihar domin kara musu kuɗaɗen shiga.

Da dama daga cikin jihohin da ke son a ba su wannan dama na ganin ita kadai ce za ta warkar da su daga dumbin matsalolin tattalin arziki.

Sannan akwai jihohin da ke cewa a ba su damar karbar kudaden harajinsu, yin hakan zai taimaka musu ba a fannin samar da ayyukan yi kadai ba, har da ci gaba da kuma rage dogaro da gwamnatin Tarayya.

Sai dai gwamnatin Tarayya na nuna turjiya kan aminta da wannan tsarin da jihohi ke daga jijiyoyin wuya a kai.

Kuɗin harajin da jihohi ke son karɓa

VAT haraji ne kan kayayyakin more rayuwa da ake iya ganinsu wanda gwamnati ke karɓa karkashin tsarin karɓar harajin haɗin-gwiwa tsakanin gwamnatin Tarayya da na jihohi da kananan hukumomi.

Jihohin da ke wannan hankoro na son a ba su damar tafiyar da haraji a kan kayayyaki wato VAT, da gwamnati ke karɓar kashi 7.5 cikin 100 kan kayayyaki.

Jihohin na son duk wani kaya ko ciniki da aka yi tsakanin yankunansu ko kuɗaɗe ya zama mallakar gwamnatin jihar domin gudanar da ayyukan ci gaba.

Gwamnatin Najeriya ta hannun hukumar tattara kuɗaɗen haraji ta tarayya take karɓar haraji a duk wani kaya ko ciniki ko ayyukan kasuwanci, sannan sai a kasafta kuɗin tsakanin gwamnatin tarayyar da jihohi da kananan hukumomi.

Sai dai wasu jihohin da ke fafutikar ganin tsarin ya sauya na cewa hakan ya saɓa dokar tattara kuɗaɗen haraji na VAT, saboda akwai cutuwa a ciki.

Jihohin Ribas da Legas da wasu sauran jihohi hudu na Najeriya ke kan gaba wajen sama wa Najeriya kashi 80 cikin 100 na kuɗaɗen harajin VAT a faɗin ƙasar.

Yadda ra’ayoyin jihohi ya bambanta kan harajin

Jihar Ribas na kan gaba gaba wajen sama wa Najeriya kashi 80 cikin 100 na kuɗaɗen harajin VAT a faɗin ƙasa

Wasu daga cikin jihohi da kawo yanzu aka ji daga gare su irin su Akwa Ibom da Adamawa sun nuna goyon-bayansu ga gwamnan Ribas, Nyesom Wike da ke son kotu ta hana gwamnatin tarayya karba ko cin moriyar wadanan kuɗaɗe na haraji.

Jihohin na ganin cewa karbar harajin da gwamnatin tarayya ke yi na rage musu ‘yanci da dogaro kan kuɗaɗen da gwamnatin ke warewa jihohi.

Wannan dalili ya sa ‘yan majalisar dokokin jiha a Akwa Ibom ke aiki kan wani daftarin doka da zai bai wa jiharsu damar tattara kuɗaɗenta na haraji.

Haka zalika jihar Legas, ta ce ita ma kudiri na gaban majalisa wanda tuni ya tsallake karatu na biyu a gaban majalisar jihar.

Sai dai gwamnatin Ekiti da Osun da Benue da Bayelsa da Gombe na cewa suna bukatar lokacin domin sake nazari kan batun don yanke hukunci.

Wata kotun tarayya a Fatakwal tuni ta bayar da umarnin cewa gwamnatin Ribas na da damar tattara kuɗaɗen harajinta.

Sai dai dukkanin waɗannan jihohi na fuskantar tsaiko daga hukumar tattara haraji ta Tarraya wato FIRS da ke kalubalantarsu har a kotu.

Hukumar FIRS ce ke da alhakin karbar kudaden haraji na VAT