Kasuwar ‘yan kwallo” Makomar Mbappe, Bellerin, Bernardo, Hodson-Odoi, Niguez
Real Madrid ta sanar da kawo karshen neman ɗan wasan PSG Kylian Mbappe, bayan da ta bayyana cewa ya yi mata tsada sosai. (RMC Sport – in French)
To amma wata majiya ta ce Madrid ta lashi takobin sayen ɗan wasan tsakiyar Rennes na Faransa da PSG ke nema.(Canal+ via Get French Football News)
Barcelona za ta nemi mai tsaron bayan Arsenal ɗan ƙasar Sfaniya Hector Bellerin, da zarar ta sayar da Emerson Royal. (Mundo Deportivo – in Spanish)
Da wahala Manchester City ta sayi ko ta sayar da wani ɗan wasa daga nan zuwa lokacin da za a rufe kasuwar cinikin ƴan wasa.
Sai dai akwai majiyar da ke cewa AC Milan ta riƙe wuta kan a sayar mata da Bernardo Silva. (Times – subscription required)
A nan kuma Chelsea ta faɗawa wakilin Jules Kounde na Sevilla cewa za ta yi wa ɗan wasan tayin ƙarshe. (ABC Sevilla, via Sport Witness)
Ita kuwa Leicester City ta nuna sha’awar ɗaukar ɗan wasan gefen Chelsea Callum Hodson-Odoi. (football.london)
A gefe guda kuma Chelsea na don ɗauko ɗan wasan tsakiyar Atletico Madrid Saul Niguez a matsayin aro.To amma Atletico na son yarjejeniyar ta zama ta din-din-din kan fam miliyan 34. (Goal)
Ɗan wasan gaban Wolverhampton Adama Traore ya ɗauko sanannen ejan ɗinnan Jorge Mendes don ya taimaka masa ƙulla yarjejeniya da Tottenham. Traore na son sake haɗuwa da tsohon mai gidansa Nuno Espirito Santo. (Footballer Insider)
Juventus ta dakatar da neman ɗan wasan tsakiyar Barcelona Miralem Pjanic, inda ta maida hankali kan Mohamed Ihattaren na PSV Eindhoven kafin a rufe kasuwa yau Talata. (Goal)
Ɗan wasan tsakiyar Chelsea Tino Anjorin na daf da zuwa Lokomotiv Moscow a matsayin aro, da nufin ƙulla yarjejeniyar zama din-din-din a ƙungiyar.(Goal)