Bayan jibgar mu da ake yi safe da yamma, ledar ruwa daya tal ake ba mutum biyu su raba duk rana – Inji Daliban Islamiyyar Tegina

Daliban Islamiyyar Tegina da ‘yan bindiga suka saki ranar Alhamis sun bayyana irin azabar da suka dandad a lokacin dsa suke tsare a hannun ‘yan bindiga.

Idan ba a manta ba ‘yan bindiga a ranar Alhamis ne yan bindiga suka sako yaran makarantar Islamiyya da suka sace kwanaki 86 da suka wuce.

A hira da wasu daga cikin yaran da iyayaen su suka yi da jaridar PREMIUM TIMES, sun bayyana yadda suka dandana azaba a hannun yan bindiga a tsawon kwanakin da suka yi a daji.

” Kwannan mu hudu muna tafiya a cikin daji sannan muka isa inda suka girke mu. kanana daga cikin mu sun dora su bisa baburan su mukuma yan manya haka muka yi ta tafiya har muka isa inda suka ajiye mu.

” Da safe dama da duka suke tashin mu daga barci. Kowa sai an lakada masa dukan tsiya sannan kuma a tashi. A bamu yar shinkafa fara da ledar ruwa daya. Mutum biyu su raba daya. Babu wanka babu wanki sai dankaran azaba da muke sha na kwanaki 86 a tsare.

Wata mata mai suna Habiba Aliyu wacce ‘ya’yan ta biyar ne aka tafi da ta bayyana jin dadin ta matuka bayan ya’yan ta sun dawo. ta kara da cewa abin da ya faru ba zai sa ya’yan ta su daina zuwa makaranta ba, ta boko da ta islamiyya.

Iyayen yara sun bayyana cewa sai da suka biya makudan kudi sannan aka saki yaran.

Hedimastar makaranta Alhassan Garba, ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun ce da kansa zai zo cancikin kungurmin daji ya tafi da yaran makarantar. Ya ce tun daga Tegina sai da yayi tafiya a cikin daji har zuwa Birnin gwari dake jihar Kaduna sannan ya karbi daliban.

A Karshe shugaban makarantar ya bayyana cewa za su karfafa tsaro a makarantar kuma suna tattaunawa da iyayen yara da sugabannin gari kan yadda za a samar da tsaron da irin haka ba zai sake aukuwa ba.