Salihu Tanko Islamiyya: Ɗaliban makarantar da aka karbo daga hannun ƴan bindiga na kwance a asibiti

‘Yan bidigar da suka sace daliban Islamiyyar nan ta Salihu Tanko da ke garin Tegina a jihar Neja sun sake su bayan shafe watanni uku suna tsare da su.

Ko da yake babu alkaluman ko nawa ne daliban da aka saki, gwamnatin jihar ta Neja ta ce za ta yi karin bayani nan gaba da zarar an kirga su.

Kimanin dalibai 136 ‘yan bindigar suka sace lokacin da suka kai wa makarantarsu hari a watan Mayun da ya gabata, amma wasu daga cikinsu sun kubuta daga baya.

Mallam Abubakar Alhassan, shi ne shugaban Islamiyyar ta Salihu Tanko da ke garin na Tegina, kuma shi ne ya yi tattaki har zuwa yankin dajin Birnin Gwari, kuma ya shaida wa BBC Hausa cewa ya zubar da hawaye saboda yanayin da ya ga yaran a ciki.

Yanayin da aka same su

Malam Abukar ya ce yaran sun yi matsananciyar rayuwa a hannun ‘yan bindigar, har ta kai ga lokacin da ya karbe su ma wasu daga cikinsu ba sa iya ko takawa da kafafunsu, yayin da wasu kuma ke aman jini.

‘”Yanayi ne mai ban tsoro, daga ni har su muna ta kuka lokacin da muka sadu, sun yi matukar jigata saboda suna cikin wata bakuwar rayuwa da ba su saba da ita a baya ba”, in ji shi.

Ya kara da cewa: “Kana ganinsu ka san yunwa ta jigata su, domin wasunsu na ta cin burodi, abin tausayi mai matukar tayar da hankali.”