Harin da aka kai a Kwalejin koyar da aikin soja ta NDA a Kaduna na iya zama siyasa : Garba Shehu

Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban Najeriya, ya ce harin da aka kai a Kwalejin koyar da aikin soja ta NDA a Kaduna na iya zama siyasa da kuma nufin kunyata gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

A ranar Talata ne wasu ƴan bindiga suka kai hari Kwalejin Sojoji da ke birnin Kaduna, kuma bayanai sun ce ‘yan bindigar sun kashe sojoji biyu sannan suka sace soja guda ɗaya yayin harin da suka kai da tsakar dare.

Harin ya ja hankali a Najeriya tare da haifar da damuwa kan karuwar matsalar tsaro a ƙasar.

Da yake mayar da martani kan harin a wata hira da gidan talabijin ta Channels ya yi da shi ranar Laraba, Malam Garba Shehu ya ce abubuwa da dama kan iya zama dalilin kai harin.

Kuma Garba Shehu wanda ya ce shugaban Najeriya ya yi Allah wadai da harin ya ce “wasu na iya kitsa harin domin kunyata gwamnatin Buhari saboda nasarorin da aka samu a yaƙi da masu tayar da ƙayar baya da kuma ƴan fashin daji.

Ya kuma ce bita da ƙullin siyasa na iya zama dalilin kai harin. 

“A yanayi na siyasa, mutane na iya amfani da wannan damar daga wannan mummunan al’amari, ba za a iya cire wannan tsammanin ba” in ji shi. 

Ya ce fadar shugaban kasar na sa ran sojoji za su yi bincike sosai domin gano abin da ya faru da dalilin faruwarsu tare da bayyana sakamakon bincikensu. 

Masu sharhi kan lamuran tsaro dai na ganin harin a matsayin wani abin kunya ga sojoji wadanda a baya, duk karfin halin dan bindiga, ba zai daddara ya kai musu hari ba.

Wasu rahotannin kafafen yada labarai na Najeriya, da ba a tabbatar ba na cewar an tsinci gawar sojan da ‘yan fashi daji suka sace a kwalejin NDA.

Amma rundunar sojin Najeriya ta ƙaryata wasu rahotannin da suka ce sojojin da ke bakin aikin tsaron Kwalejin Horon Sojoji ta NDA bacci suke lokacin da ƴan bindiga suka kai hari wanda ya kai ga kashe sojoji biyu da sace soja ɗaya.

Sanarwar da babban jami’in yaɗa labarai na rundunar sojin ya fitar Manjo Janar Benjamin Olufemi Sawyerr ya ce labarin da jaridar Cable ta wallafa ba gaskiya ba ne inda ya ƙalubalanci jaridar ta bayar da shaidar da ke tabbatar da jami’an sojin suna bacci lokacin da ƴan bindigar suka kawo hari.

Labarin da ake yaɗawa na cewa bacci ne ya kwashi jami’an da ke kula da kamarori na tsaro lokacin da ƴan bindigar suka abka kwalejin NDA.

Rundunar sojin ta ce babban hafsan sojin Najeriya da hukumomin NDA sun kaddamar da bincike domin gano yadda har aka samu matsalar da ta ba ƴan bindiga damar shiga kwalejin.