Gwamnatin Kano ta haɗa kai da Faransa don haɓaka noma

Gwamnatin Jihar Kano da ke arewacin Najeriya za ta ƙulla yarjejeniya da Faransa domin haɓaka harkokin noma a jihar. 

Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya bayyana hakan yayin da yake karɓar baƙuncin jakadan Faransa a Najeriya, Jérôme Pasquier, ranar Litinin a Kano.

Ganduje wanda mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta, ya ce haɗin gwiwar za ta samar da sabbin hanyoyin bunƙasa tattalin arzikin Kano. 

Gwamnan ya gode wa Faransa bisa ƙaddamar da aikin tituna a ƙauyuka sannan ya buƙaci masu zuba jari da “su nemi arziki a Kano ta hanyar bincika albarkatu na ɗan Adam da kuma na Allah da ke jihar”. 

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito Mista Pasquier yana cewa ya je Kano ne “domin haɓaka alaƙa tsakanin Najeriya da Faransa”. 

“Kano babbar kasuwa ce kuma mai matuƙar muhimnmanci gare mu,” in ji shi.