KISAN GILLAR MATAFIYA A JOS: Sunayen waɗanda aka kashe

Kwana ɗaya bayan mummunan kisan da matasan Kiristocin Jos su ka yi wa Musulmai matafiya a Jos, jaridar HumAngle mai bada bayanan al’amurran da su ka shafi matsalar tsaro a Arewacin Najeriya, ta buga sunayen matafiya su 22 da aka kashe a yayin harin.

HumAngle ta ƙara da cewa wani da ya tsira da ran sa daga iyalin Alhaji Baido da aka kashe a cikin motar, ya ce baya huɗu da aka kashe, har yanzu su na cigiyar wasu iyalin Alhaji Baido ɗin su uku da ba a ji ɗuriyar halin da su ke ciki ba.

Jerin Sunayen Waɗanda Aka Kashe:

1. Sule Alhaji Baido

2. Malam Ahmadu

3. Siddi Abubakar

4. Abdulkarim Mumini

5. Malam Suleiman

6. Malam Salihu Halilu

7. Malam Muhammadu

8. Malam Bello Ori

9. Hamidi Malam Musa Shehu

10. Malam Abdulkarim

11. Alhaji Abubakar Lawal

12. Alhaji Rugga

13. Baa Alhaji Bayo

14. Gambo Alhaji Baido 

15. Alhaji Usman Lolo Shagari

16. Malam Maude Alhaji Ɓaido

17. Ibrahim Haruna

18. Malam Muhammadu

19. Halilu Hunter

20. Yakubu Malam Bello

21. Malam Isyaku

22. Sai waɗansu mutum huɗu da ba a gane su ba.

Sarkin Musulmi ya roƙi kada a yi ramuwar-gayya.

Majalisar Zartaswar Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta yi gargaɗi da roƙon cewa kada Musulmai su yi ramuwar-gayyar kisan da aka yi wa Musulmai a hanyar Rukuba, cikin Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a ranar Asabar.

An kashe matafiyan waɗanda dukkanin su Fulani ne Musulmai da PREMIUM TIMES HAUSA ta bada rahoto su 22 a lokacin da su ke kan hanyar komawa jihar Ondo inda su ke da zama, bayan sun halarci taron Maulidin murnar shiga Sabuwar Shekarar Musulunci a gidan Sheikh Ɗahiru Bauchi, a Bauchi.

Sai dai kuma wasu rahotanni da ke ƙara fitowa sun bayyana cewa waɗanda aka kashe ɗin sun fi 22, domin an ƙara samun waɗansu gawarwakin daga baya.

Cikin wata sanarwar da NSCIA ta fitar ɗauke da sa hannun Darakta Zubairu Usman-Ugwu, Majalisar ta yi kiran da hukumomin tsaro su tabbatar da sun kamo dukkan waɗanda ke da hannu wajen wannan mummunan kisan gilla da aka yi.

Sai dai kuma ta ce har yanzu ana cigiyar wasu mutum takwas da ba a ji halin da su ke ciki ba, ko da rai ko babu.

NSCIA ta miƙa ta’aziyya da alhinin ta ga Sheikh Ɗahiru Bauchi da kuma iyaye da iyali da ‘yan’uwan waɗanda aka kashe.

Tuni dai Shugaba Muhammadu Buhari da Gwmna Simon Lalong na Jihar Filato su ka yi tir da wanann kisan.

CAN Ta Yi tir Da Kisan, Ta Nemi A Zaƙulo Makasan:

Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta nuna rashin jin daɗi da matuƙar ba baƙin cikin kisan da wasu matasan Kiristoci su ka yi wa Musulmai matafiya a Rukuba, kusa da Jos, a ranar Asabar.

Cikin wata sanarwa da Shugaban CAN na Jihar Filato, Polycap Lubo ya fitar a ranar Lahadi, ya ce abin takaici ne kisan da aka yi wa matafiyan, kuma ya yi kira da jami’an tsaro su zaƙulo waɗanda su ka aikata wannan mummunar ɓarna.

Yayin da Polycap ya ce babu wani dalilin da zai sa a riƙa kashe rayukan mutane saboda bambancin ƙabila ko addini, ya kuma yi tir da kashe-kashe da tashin hankalin da ke faruwa a Ƙananan Hukumomin Bassa, Riyom, Jos ta Kudu da kuma Barkin Ladi.

An Ƙaƙaba Dokar Hana Fita A Jos Ta Arewa, Ta Kudu Da Kuma Bassa:

Gwamnatin Jihar Filato ta ƙaƙaba dokar hana fita awa 24 a baki ɗayan Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna Simon Lalong, Makud Macham ya fitar, ya ce a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa an hana fita daga safiya har zuwa wata safiyar, tun daga ranar Lahadi, 15 Ga Agusta, 2021.

A Ƙananan Hukumomin Jos ta Kudu da Bassa kuma an hana fita daga ƙarfe 6 na safiya zuwa ƙarfe 6 na yamma.

Ya ce Gwamna Lalong ya yi haka ne domin hana ƙara ɓarkewa ko fantsamar kashe-kashe a wasu yankunan ƙananan hukumomin.

An Kama Mutum 20, Ana Neman Sauran:

Rahotanni da kuma kafafen yaɗa labarai sun ruwaito jami’an tsaron Jihar Filato sun bayyana damƙe mutum 20 daga cikin waɗanda ake zargin sun tare hanya a Rukuba da ke Jos, su ka kashe matafiya fiye da 22.

Idan ba a manta ba, Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaro su tabbatar sun kamo dukkan masu hannu a wannan mummunan kisa, domin a hukunta su.

Majalisar Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA) da Gwamnatin Jihar Filato da CAN da sauran miliyoyin ‘yan Najeriya na ci gaba da yin kira a tabbatar an kamo waɗanda su ka yi kisan domin a hukunta su.

Hasalallu na ci gaba da cewa hukunta waɗanda su ke aikata kisan gilla a kan jama’a ne kaɗai zai iya magance ramuwar-gayya.