Kamfanin Shell zai biya ƴan Najeriya da ya gurbatawa muhalli cikin shekaru sama da 50 dala miliyan 111.

Shell za ta biya diyyar $111m kan malalar man shekarun 1970 a Najeriya

Kakakin kamfanin ya ce kuɗaɗen da za su biya zai warware taƙaddamar da ke tsakanin kamfanin da al’ummar Ejama-Ebubu kan gurɓata musu muhalli a lokacin yakin Biafara tsakanin shekarar 1967 zuwa 1970.

Kamfanin ya ce gurbacewar muhallin ya faru ne ta hanyar mutanen da yake mu’amala da su.

A shekara ta 2010 wata kotu a Najeriya ta ci tarar Shell din dala miliyan 41.36, sai dai kamfanin ya yi ta ɗaukaka ƙararrakin da bai yi nasara ba.

A bara, Kotun Ƙolin ƙasar ta ce, idan aka haɗa da kuɗin ruwa, tarar da aka cin kamfanin ta nunka na hukuncin shari’ar farko sau 10, ko da yake Shell ya musanta hakan. A shekarar 1991 ne aka fara shigar da ƙarar.

A baya Shell ya ce ba a ba shi damar kare kansa kan tuhume-tuhumen da aka yi masa ba, inda ya fara ɗaukaka ƙara a kotun ƙasa da ƙasa a farkon shekarar nan.

Kamfanin dillancin labaran AFP ta ruwaito lauyan da ke kare al’ummomin da aka gurɓata wa muhallin Lucius Nwosa, na cewa “Dabara ta ƙare musu sai suka miƙa wuya. An cimma nasara ne saboda jajircewar al’ummomin wajen neman haƙƙinsu.”

Duk da cewa an shafe tsawon shekaru ana wannan shari’a, har yanzu gurɓatar muhalli sakamakon malalar mai daga bututai na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar yankin Neja-Delta

A farkon wannan shekara, a wani lamarin daban, wata Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Netherlands ta yanke hukunci cewa Kamfanin Shell na Najeriya ne ya jawo gurɓacewar malalar a yankin Neja Delta daga shekarar 2004 zuwa 2007.

Kotun ta bai wa Shell Nigeria umarnin biyan manoman yankin diyya, yayin da aka bai wa uwar kamfanin na Anglo-Dutch umarnin dasa na’urorin da za su kare afkuwar hakan a gaba.

Wata ƙungiyar manoma a shekarar 2008 ta shigar da ƙarar, inda take zargin cewa an jawo mummunar gurbatar muhalli.

Shell ya musanta cewa malalar ta faru ne a sakamakon zagon ƙasa.