“Talauci ya sa mijina ya tura ni yin bara Kano ni da ‘ya’yana hudu”
A baya-bayan nan ana samu yawaitar mata masu bara a kan tituna a birnin Kano, da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Matan dai a lokuta da dama suna tafe ne tare da ‘ya’yansu kanana da ‘yan mata, a kowane lokaci suna yini har ma da daddare.
Wannan lamari yana dasa ayar tambaya a zukatana mutane, kan ko daga ina suka fito, kuma me suke son cimma?
Daya daga cikin irin wadannan mata da Halima Umar Saleh ta ci karo da ita a kwanakin baya a Kano, ta shaida mata cewa talauci ne ya yi wa mijinta katutu sai ya ce “ta shiga duniya neman abinci ita da ‘ya’yanta hudu.”
Mata wacce ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce ta fito ne daga garin Gumel na jihar Jigawa mai maƙwabta da Kano.
“Wallahi talauci ne ya yi mana yawa, sai mijina ya ce ya yarje min na tafi ko ma ina ne don neman abin da za mu dinga ci ni da ‘ya’yana.
“Ni kuma sai na ga babu garin da ya fi dacewa na je sai Kano, don ita ce tumbin giwa, kuma na Allah ba sa karewa, na tabbata ba zan rasa abin da za mu ci ba da ‘ya’yana,” in ji ta.
Da aka tambaye ta ko ina danginta da har ta bar mahaifarta da tarin yara suka taho Kano, sai ta ce “to yanzu zamani ya sauya kowa ta kansa yake yi, babu mai kula ni da gayyar ‘ya’yana.”
“Mijina kuma tun da na taho dai ba mu gana ba, amma da yake ban daɗe da tahowa ba shi ya sa.
“Idan dai har na samu tallafin da nake so to gaskiya zan koma gida don ba zan iya ci gaba da zama a nan ba,” a cewar matar.
Wannan lamari dai ba a saba ganin irinsa ba a ƙasar Hausa, a ce miji ya bai wa matarsa izinin zuwa ko ina a duniya don neman abinci saboda “gazawarsa.”
Sai dai wasu na danganta hakan da halin ƙa-ƙa-ni-kayin da aka samu kai a ciki a mafi yawan yankunan ƙasar.
Amma ga wasu, hakan ya saɓawa tsarin addini da al’ada.
A ina ta ke rayuwa ?
A kowace safiya wannan matar ta kan bar masauƙinta ne da ke Giginyu inda wata mata ta ba ta dan wajen da take kwana ita da ‘ya’yanta. Ta kan shiga gari suna yawo daga wannan kwararo zuwa wancan titi don neman abin da za su ci.
A mafi yawan lokuta sun fi rabewa ne a kusa da kantunan sayar da abinci ko na kayan masarufi don a ba su ragowar da masu saya suka ci ko kuma a ba su sadakar kudi.
A wannan yammaci mai cike da hadari matar tana rakube a jikin wani kantin sayar da abinci ita da ‘ya’yanta uku mata sai karamin namiji a goye.
Ga dukkan alamu ta ukun da na hudun ratansu babu yawa don dukkansu biyun sai tsala kuka suke yi.
“Sau tari ma haka muke komawa gida ba mu koshi ba, wasu lokutan kuma sai a dace mu samu da dan dama har mu yi guzurin wanda za mu ci da daddare.
Ta ce da kafa suke yin duk wannan yawon, idan ruwa ya sauko kuwa sai su samu jikin katanga ko wani ginin da ba kowa su rabe har sai an gama.
‘Ya’yan wannan mata manyan na farko mai shekara 12 da mai shekara 10 da ya kamata a ce suna makarantar arabiya da ta boko, da su ake wannan fafutuka, kuma babu wani kyakkyawan fatan cewa an tanadar musu rayuwa mai kyau a gaba.
A lokuta da dama ma a kan ga irin wadannan mata da ‘yan mata suna goge gilasan mota a kan tituna, abin da aka fi ganinsa a tsakanin maza.