MATSALAR GARKUWA DA MUTANE NA YI WA KANO BARAZANA
Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da ‘danuwan Minista Sabo Nanono a day ago 4101 views by Muhammad Malumfashi – ‘Yan bindiga sun shiga gidan gadon Ministan harkar gona, Sabo Nanono – Rahotanni sun ce an yi nasarar tserewa da wani ‘danuwan jinin Ministan – Ana fama da matsalar garkuwa da mutane musamman a yankin Arewa Wasu miyagu da ba an sa ko su wanene ba, sun shiga gidan dangin Ministan harkar gona na Najeriya, Muhammad Sabo Nanono. Jaridar Sahelian Times ta fitar da rahoto cewa ‘yan bindigan sun yi nasarar tsere wa da wani ‘danuwan Ministan, Babawuro Tofai. An sace ‘danuwan Ministan gonan ne a ranar Lahadi, 22 ga watan Nuwamba, 2020, cikin dare.
‘Yan bindiga sun je gidan wani ‘Dan Majalisa a Katsina Zuwa lokacin da ake fitar da wannan rahoto a yammacin ranar Litinin, babu tabbacin su wanene su kayi wannnan danyen aiki. Ana zargin cewa harin ba zai wuce na garkuwa da mutane ba a daidai lokacin da ake fama da yawaitar sace-sacen Bayin Allah. A ‘yan kwanakin nan, jama’a a Arewa suna fuskantar baranzanar garkuwa, inda ake tsare Bayin Allah har sai an karbi kudin fansa. Da aka tuntubi mai magana da yawun bakin jami’an ‘yan sanda na Kano, Abdullahi Haruna, ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin.
DSP Abdullahi Haruna ya ce ‘yan sanda na reshen jihar Kano suna duba halin da ake ciki, kuma sun fara bincike domin bankado laifin. Kawo yanzu, Mai girma ministan gonan bai fito ya ce wani abu ba tukun tun da labarin shiga gidan gadon nasu ya fito a ranar Litinin. A makon yau ne kuma aka wayi gari da labarin cewa wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki rukunin gidajen malaman jami’ar ABU da ke Zaria. A dalilin haka miyagu su ka yi awon gaba da wani Farfesa. Wannan ne karo na biyu da ake samun labarin garkuwa da mutane a jami’ar.