An Kaddamar Da Bincike Kan Sojan Da Ya Kashe Wani Matashi a Jos

Rundunar tsaro ta musamman a jihar Filato ta damke wani jami’inta don gano dalilin da ya sa ya harbe wani matashi dalibin jami’ar Jos dan shekara ashirin da haihuwa a shelkwatar shiyya ta daya ta rundunar da ke garin Jos.

A wata sanarwa da aka fidda mai dauke da sa hannun jami’in hulda da manema labarai na rundunar ta STF a jihar Filato, Manjo Ibrahim Shittu, ta ce ta samu rahoton ayyukan barayi da ‘yan kungiyar asiri a yankin Holshe a karamar hukumar Jos ta Kudu, musamman a lokacin da gwamnati ta sanya dokar hana fita don dakile yaduwar annobar coronavirus. 

Sanarwar ta kuma ce jami’an sojin sun kama matasa bakwai bisa bayanan da suka samu amma da suka gudanar da bincike sun gano cewa biyar daga cikinsu basu da laifi sai suka sake su, amma kafin su fita daga harabar shelkwatar sai wani jami’in soja ya harbe daya daga cikin matasan mai suna Rinji Bala akan cewa ya yi zaton zasu gudu ne.

Shugaban kungiyar raya matasan Angas, Mr. Nensok Gonet ya ce wannan shine karo na biyu da sojoji ke kashe masu ‘yan uwa ba tare da wani kwakkwaran dalili ba. Ya kuma bukaci gwamnati ta dauki duk matakin da ya kamata wajen gudanar da bincike.