Lionel Andres Messi

An haifi Lionel Messi a cikin Rosario a Argentina, ranar 24 ga Yuni 1987. Mahaifinsa ma’aikaci ne na karfi, kuma mahaifiyarsa mai share-share ce. 

Ya fara wasa tun yana dan karami, sannu a hankali baiwarsa na kwallon kafa  ta bayyana yana dan shekaru 11,

messi a shekaru 11

Sau da yawa ana kwatanta shi a matsayin wanda zai maye gurbin Diego Maradona saboda irin kwalakwalan da yake zira wa a raga da kuma murƙushe abokan hamayyarsa a filin daga.

Danwasan(Messi) ya taso tun yana karami dauke da cutar nan GHD wato (Growth Hormone Deficiency), amman kasancewar ya taso cikin dangi masu rauni ta fuskar kudi, Wannan wani yanayin ne wanda ya kawo cikas kuma yana buƙatar magani mai tsada.

Kulob din sa na gida, wato River Plate sun nuna sha’awar su ga Messi amma ba sa son su biya kudin magani. Dukda haka, Messi ya bukaci gwaji tare da Barcelona, ​​kuma kocin Carles Rexach ya yi sha’awar – ya ba da Messi kwangila Wanda ya haɗa da biyan magani don kula da Messi a Spain kuma an rubuta yarjejeniyar a kan  takarda.

Messi Katolika ne, amma mutum ne mai ra’ayin ko’inkula akan  addini, abin ban sha’awa, wata kungiyar labarai ta Musulunci ta ba da rahoton cewa Messi ya musulunta, amman ba a tabbatar da tushen labarin ba, kuma Messi bai ma damu da yin magana game da hakan ba.

Ya kwashe tsawon rayuwarsa yana aiki tare da Barcelona, ​​inda ya lashe kofuna sama-da-34, 

*wadanda suka hada da La Liga goma,

*Kofin Zakarun Turai hudu

*Copas del Rey shida,

*Supercopa de Españashida

*UEFA Super cup uku

*Da kuma FIFA cup karo uku

A kasar sa kuwa ta Agentina,

  • Ya samu Kambun Olympic Gold Medal: 2008
  • Ya daga kofin FIFA Under-20 World Cup: 2005
  • A 2006 World Cup kuwa ya dangana ga matakin Quarter Final
  • Haka ma a 2010 World Cup, shima ya dangana ga matakin Quarter Final Haka ma ya samu Halattar 2014 World Cup
  • Hakazalika ya samu halattar kofin zakarun Duniya na 2018

Messi ya kasance mai burin halattar wasu kungiyoyin kwallon kafa tare da kashe kudi masu yawa, amma ya kasance mai biyayya ga kungiyar kwallon kafa ta Barcelona. 

Yana daya daga cikin ‘yan kwallo mafi tsada a duniya. An kiyasta albashinsa na asali a Euro miliyan 40 a shekara. Wannan ya sa ya zama tauraron wasanni mafi tsada – in ji Jaridar Forbes. Albashinsa na mako-mako da yake samu a Barcelona shine $ 667,000 a kowace mako.

Messi yana da salon rayuwa mai zaman kansa da son rayuwa mai kyau. hadaddiyar gidan sa yana garinsu na Rosario, kuma gidan yana daga jerin gidaje 7 masu tsada a Duniya, mutum ne ma’abocin son Kare, a bangaren motoci kuwa abin ba Magana, yana hawa motoci na gani na fada a duniya irin su Bugatti wacce darajarta takai Doller miliyan biyar da Digo 8 (5.8), ga kuma Mini cooper wacce darajarta takai Doller Miliyan $29,900,00  harda irnsu Dodge, Audi da kuma Maserati wacce farashin ta ya kai doler 181,183Yana da mata ‘yar kasar Argentina mai suna Antonella Roccuzzo, kuma suna da’ ya’ya biyu.