2023: Dama zuwa kai ka kula da lafiyarka, Kwankwaso ya shawarci Tinubu

Ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya shawarci abokin karawarsa a zaɓen 2023, Bola Ahmed Tinubu, da ya kula da lafiyarsa gabanin shiga zaɓen.

Kwankwaso, wanda tsohon ministan tsaro ne kuma wanda ya mulki jihar Kano sau biyu, yayin wata hira da gidan talabijin na Arise News a jiya Lahadi, ya ce kamata ya yi Tinubu ya kula da lafiyarsa, inda ya yi gargadin cewa yakin neman zaɓen 2023 zai kasance mai wahala.

“Idan ka ga abokina Bola, ka ce masa ya bi a sannu, ya kula da lafiyarsa sosai… saboda ina sonsa sosai, abokina ne.

“Wannan yaƙin neman zaɓen zai yi tsauri sosai. Ya na buƙatar jajircewa sosai da dai sauransu.

“Ina fatan zai yi sauki domin mu ci gaba da fafutukar tabbatar da kasa ɗaya mai ƙarfi da wadata a Nijeriya,” in ji Kwankwaso.

Da aka tambaye shi ko Tinubu na masa barazana, Kwankwaso, wanda shi ne mataimakin kakakin majalisar wakilai a jamhuriya ta uku, ya ce Tinubu a matsayinsa a kashin kansa mutumin kirki ne, inda ya ƙara da cewa bai san abin da Tinubun zai yi daban da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

“Damuwata kawai ita ce jam’iyyar da ya fito. Na san shi mai dabara ne; Bola Tinubu, mutumin kirki ne. Na zauna tare da shi sau da yawa ba za a iya kirgawa ba daga 1992 zuwa yau.

“Ina fatan idan na gan shi zan tambaye shi me zai gaya wa ‘yan Nijeriya abin da zai yi na daban da abin da Muhammadu Buhari ke yi a yau.

“Wannan ita ce babbar damuwata a gare shi. Idan ba yi nasara ba, zan iya ba shi shawara amma zai zama kamar gina wani abu ne bai mai billewa ba.

“Idan na gan shi, zan yi masa fatan alheri ko kuma idan kun gan shi, ku ce masa ina yi masa fatan alheri – amma ya bi a sannu,” in ji Kwankwaso.