Ƙungiyar ƙwadago ta dakatar da zanga-zangar ƙasa kan cire tallafin mai

NLC

Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya ta Nigeria Labour Congress (NLC) ta dakatar da zanga-zangar ƙasa da kuma ta jihohi da ta shirya gudanarwa game da janye tallafin man fetur. 

Matakin ya zo ne ‘yan awanni bayan ƙungiyar ta sha alwashin ci gaba da tattara kan ‘ya’yanta don gudanar da zanga-zangar daga Alhamis mai zuwa kafin daga baya gwamnati ta sanar da soke cire tallafin. 

Shugabannin ƙungiyar sun ce za su ci gaba da tattaunawa da gwamnati kan batun gyara matatun mai na cikin gida da samar da ayyukan yi da kuma farashin mai mai sauki ga ‘yan ƙasa. 

“Biyo bayan matakin gwamnati na janye maganar cire tallafin mai, majalisar zartarwa ta NLC ta gana ta bidiyo a yau (Talata) don duba matakin,” a cewar Shugaban NLC Ayuba Wabba a wajen taron manema labarai. 

“Majalisar ta ɗauki matakin jingine zanga-zangar ƙasa ranar 27 ga watan Janairu da kuma ta jihohi da aka shirya farawa ranar 2 ga Fabarairu.” 

Gwamnatin Shugaba Buhari ta ce za ta ci gaba da biyan tallafin har zuwa nan da wata 18, yayin da wa’adin gwamnatin zai ƙare wata biyu kafin haka.