Gwamna Babagana Umara Zulum ya jagoranci tawagar sanatocin Borno inda suka gana da babban hafsan tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor a hedikwatar tsaro da ke Abuja.
Tawagar sanatocin ta ƙunshi Kashim Shettima mai makiltar Borno ta tsakiya da Muhammad Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu da Abubakar Kyari mai wakiltar Borno ta arewa.
Sanarwar da Isa Gusau ya fitar ta ce shugabannin jihar ta Borno sun yi ganawar sirrin ce ranar Litinin da babban hafsan sojin Najeriya kan sabbin hare-hare da sace-sacen da kungiyar ISWAP ke yi, musamman a kudancin jihar.
“A zaman tattaunawar na tsawon sa’a ɗaya, Zulum da ‘yan majalisar dattawa sun fito fili sun bayyana muhimman batutuwan da suka dame su kan kalubalen tsaro da ke addabar jihar Borno da kuma buƙatar a gaggauta daƙile barazanar hare-hare da sace-sacen jama’a sassan jihar.
“Taron ya yanke shawarar ɗaukar matakan da ba a bayyana ba kan batun inganta harkokin tsaro a fadin jihar,” in ji sanarwar