Kasar China ta yi alkawarin bai wa Afirka alluran rigakafin cutar Covid-19 biliyan daya, yayin da nahiyar ke fafutukar yadda al’ummominta za su samu cikakkiyar rigakafin.
A jawabin da ya yi na taron kasashen Afirka da kasar ta China, wanda ke gudana a Dakar babban birnin kasar Senegal, shugaba Xi Jinping ya ce, kasarsa za ta ba da gudummawar allurai miliyan 600 kai tsaye.
Karin allurai miliyan 400 za su fito daga wasu hanyoyin, kamar saka hannun jari a wuraren samar da kayayyaki, wadanda ba su da yawa a yawancin Afirka.
Wa’adin na Xi ya zo ne a wani bangare na dandalin tattaunawa tsakanin Chaina da kasashen Afirka tare da mai da hankali kan harkokin ciniki da tsaro, da dai sauransu.
Kasar China dai na zuba jari sosai a Afirka, kuma ita ce babbar abokiyar kasuwanci a nahiyar, inda ta zuba jari da ya kai Dalar Amurka biliyan 200 a shekarar 2019, a cewar ofishin jakadancin kasar China da ke Dakar.
Bincike ya nuna cewa akwai karancin wadanda suka karbi rigakafin sosai a nahiyar Afirka, idan aka kwatanta da sauran kasashen duniya, inda kasashe da dama ke kara kaimin neman taimakon kasashen waje saboda rashin kayayyakin da ake samarwa a cikin gida.
Taron da aka yi a Senegal ya biyo bayan ziyarar da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya kai kasashen Kenya, Najeriya da kuma Senegal a wannan watan