Wani kudurin doka da zai sa a rika cin tarar jamia’n gwamnnati da suka fita neman magani kasar waje da kudin gwamnati ba tare da izini ba, naira miliyan 500 ya wuce domin karatu na biyu, a majalisar Wakilan Najeriya.
Kudurin na neman a yi sauyi ne a dokar kula da lafiya ta kasar ta 2014, ta yadda dokar za ta kunshi hukuncin da za a yi wa duk jami’in da ya saba tanade-tanadenta.
Dan majalisa Sergius Ogun wanda ya gabatar da kudurin ya ce ya yi hakan ne da nufin rage yawan tafiye-tafiye zuwa kasar waje da jami’an gwamnati ke yi domin neman lafiya, su yi watsi da asibitocin kasar.
Mista Ogun ya ce matakin zai sa a mayar da hankali sosai wajen gyar