X

Za a hukunta Alkalan shari’ar Kano

Abuja – Majalisar NJC da ke kula da Alkalai ta shira yin bincike game da abin maganar da aka jawo a shari’ar zaben gwamnan jihar Kano.

Daily Trust ta ce kura-kuren da aka samu a takardun hukuncin CTC na shari’ar zaben gwamnan Kano ya jawo majalisar NJC za tayi bincike.

Jami’an NJC wanda su ke da alhakin korar Alkali idan ya yi laifi sun tabbatar da haka lokacin da su ka ziyarci manema labarai a garin Abuja.

Wani jami’in majalisar ya shaidawa cewa sun samu korafe-korafe a kana bin da ya faru a shari’ar Kano, kuma za a dauki matakin da ya dace.

A cewarsa, za a shirya cikakken bincike ta hanyar kafa kwamiti na musamman, sannan a zartar da hukunci kamar yadda dokar NJC ta tanada.

Wani mataki Abba Kabir Yusuf ya dauka? Babban jami’in yake cewa duk da lauyan Abba Kabir Yusuf ya ce za su kai maganar zuwa kotun koli, wannan ba zai hana NJC yin bincikenta ba

Su wanene Alkalan shari’ar Kano? Mai shari’a Moore Aseimo Abraham Adumein ne shugaban zama a shari’ar da Abba Kabir Yusuf ya dauka zuwa kotun da ke zama a garin Abuja.

Baya ga da ke kotun daukaka kara da ke garin Ibadan, Bitrus Gyarazama Sanga da Lateef Adebayo Ganiyu na cikin alkalan shari’ar zaben na 2023.

Wata majiya ta ce ana zargin Alkalan sun sa hannu a takardun CTC ne ba tare da karanta abin da ya kunsa ba, don haka dole za a hukunta su.

APC tayi nasara a Kano ko NNPP? Da aka fitar da takardun dauke da kura-kurai, gwamnatin Kano ta ce ba a tsige ta ba, an rahoto Kwamishinan shari’a ya na cewa APC aka doke.

Ko kafin takardun hukuncin su fito, an ji sai da kotun ta dauki lokaci mai tsawo. Wasu su na ba alkalai uzuri aikin da ke kansu ne ya yi yawa.

Categories: Labarai
Tags: labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings