X

‘Yan ta’adda sun kashe mutum biyu sun sace 30 a Birnin-Gwari

‘Yan ta’adda sun sake kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu kusan 30 a wasu kauyukan karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.

Wani wanda ya tsira da ransa, Malam Isa ya ce al’ummomin da abin ya shafa sun hada da Shiwaka, Unguwan Bagudu da Sabonlayi.

A cewar Isa, za a samu karin gawarwaki a cikin dazuzzuka idan an gudanar da cikakken bincike.

Al’ummar yankin, a cewarsa, ba za su iya biyan harajin da ‘yan fashin suka dora musu ba, shi ya sa aka kai wa al’umomin hari.

Ya bayyana cewa, “Sun kai harin ne a ranar Litinin da misalin karfe 11:30 na safe yayin da akasarin mutane suka je gonakinsu. Wannan ne wa’adin harajin da ‘yan fashin suka sanya.”

Ya yi kira ga gwamnatin shugaba Bola Tinubu da ta magance matsalar ‘yan fashi da makami.

Ya koka da cewa, “ko da an biya harajin, ‘yan fashin ba za su daina kai hare-hare a kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.”

Categories: Labarai
Tags: labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings