Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi tare da hadin gwiwar Ahmed Ali Kwara Hunters Squad sun yi nasarar kashe wasu mutane biyar da ake zargi da yin garkuwa da mutane tare da kwato bindigogi a karamar hukumar Giade ta jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Auwal Muhammad Musa ne ya bayyana haka a ranar Litinin da ta gabata yayin da yake zantawa da manema labarai a sashin karamar hukumar Giade.
Ya ce, “daga sakamakon hadin gwiwa da hukumomin tsaro da abin ya shafa, a ranar 11 ga Fabrairu, 2024, da misalin karfe 0200, bayanan da rundunar ta samu sun nuna cewa wasu mutanen da ba a san ko su waye ba, wadanda ba su gaza biyar ba, dauke da AK-47. bindigu, sun mamaye karamar hukumar Giade da nufin sace mutanen da ba su ji ba ba su gani ba na yankin.”
CP ya ce da samun labarin, wata tawagar jami’an tsaro tare da hadin gwiwar ‘yan kungiyar farauta ta Ahmed Ali Kwara, sun yi gaggawar kai dauki tare da yin artabu da wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne a cikin wani fadan bindiga. Sakamakon haka, an kawar da duk wadanda ake zargi da aikata laifin nan take.
Musa ya bayyana cewa binciken farko ya gano cewa wadanda ake zargin sun yi garkuwa da wani Abdullahi ne, wanda ba a sani ba, daga jihohin Bauchi da Taraba ne ya gayyace su.
“Bugu da ƙari kuma, masu garkuwa da mutane ƴan ƙungiyar ne da suka yi garkuwa da Emeka na Itas-Gadau a wani lokaci a shekarar 2023 kuma suka karɓi Naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa,” in ji shi.