X

‘Yan Sanda Sun Kama Mashawarcin Masu Garkuwa Da Mutane a Jihar Neja

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta kama wani mutum da ta ce yana taimaka wa masu garkuwa da mutane ta wajen basu shawarwari. 

Shi dai mutumin ya zamana ne ‘mai ba da shawara ta sihiri ga gungun masu garkuwa da mutane a tsakanin jihar Neja da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.

A bisa rahoton leken asiri, jami’an jihar da ke da alaka da rundunar ‘yan sandan sun kuma dakile shirin yin garkuwa da wasu masu ibada a wata Coci da ke kauyen Buku a karamar hukumar Abaji a babban birnin tarayya Abuja kamar yadda wadansu majiyu a Najeriya su ka bayyana.

Wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO), DSP Wasiu A Abiodun, a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar, ta ce wanda ake zargin a lokacin da ake yi masa tambayoyi ya amsa cewa shi ne jagoran ayyukan sihiri ga wasu mashahuran ‘yan bindiga da ke addabar jihohin arewa ta tsakiya; Niger, Birnin Tarayyar Abuja da jihar Nasarawa.

Categories: Labarai
Tags: HAUSAlabarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings