Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta haramta zanga-zanga a fadin jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mohammed Usain Gumel ne ya bayar da wannan umarni bayan ‘yan jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) mai mulki da jam’iyyar adawa ta APC sun bukaci mambobinsu da su yi ta kwarara kan tituna kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa bangaren shari’a.
Kwamishinan ya ce duk wani yunkuri na rashin mutunta dokar za a dauki shi a matsayin wani laifi ga tsaron kasa.
Ya ce, “Don haka jama’a su lura da saninmu cewa jam’iyyun APC da NNPP a halin yanzu suna ta tara jama’a na haya da sunan jam’iyyar Civil Society Coalition kuma ba tare da izini daga shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya ba, ba tare da amincewar hukumomin tsaro a jihar ba.
“Ya kamata masu shirya taron da na kungiyar su lura cewa duk wani yunkuri na rashin mutunta kungiyar NLC da hukumomin tsaro a jihar, ta hanyar yin wasa a kan tabarbarewar yanayin tsaro, wanda hadin gwiwar hukumomin tsaro ke gudanarwa, ba wai kawai rashin zaman lafiya ba ne, laifi ne kuma har ma Laifin da ya shafi Tsaron Kasa 3. Ya zuwa yanzu wannan hukumar ‘yan sanda ta gudanar da bincike kuma ya nuna cewa wasu ‘yan jam’iyyun siyasa biyu ne da suka kasance.
“Daga karshe, rundunar ‘yan sandan tana godiya da dimbin goyon baya da hadin kai da take samu daga al’ummar jihar domin samun zaman lafiya, tsaro, kwanciyar hankali da kuma moriyar kowa.”