X

Yan sanda sun ceto fasinjoji 16 da aka yi garkuwa da su a Kogi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP William Aya ya fitar ranar Litinin.

Aya ta ce aikin ceton ya biyo bayan sace fasinjoji 11 daga motar Peace Mass Transit Bus da wasu biyar daga wata motar bas Sienna da ke kan titin Ette Enugu Ezike a ranar 25 ga Fabrairu, 2024.“

Rundunar hadin gwiwa ta ‘yan sandan Kogi da sojoji daga jihar Enugu sun yi gaggawar kai dauki, inda suka ceto duk wadanda lamarin ya rutsa da su daga daji ba tare da jin rauni ba,” inji shi.Ya kara da cewa “ana ci gaba da kokarin cafke wadanda ake zargin tare da hukunta su.”

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Bethrand Onuoha, yayin da ya yabawa rundunar hadin guiwar jami’an tsaro, ya jaddada aniyar rundunar na ci gaba da kai hare-hare kan masu aikata laifuka a jihar.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da hada kai da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro wajen tabbatar da isassun tsaron rayuka da dukiyoyi.

Categories: Labarai
Tags: labarai
Umar Muhammad:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings