X

‘Yan Nijeriya 802 da suka makale a Saudiyya za su dawo yau.

Wasu ‘yan Najeriya da aka kame a kasar Saudiyya da laifin haure ba kan ka’ida ba zasu dawo Najeriya yau – A yau Alhamis, ana sa ran dawowar kimanin ‘yan Najeriya sama da 800 a Abuja – Ana kuma sa ran dawowar sauransu a jirgi na biyu a ranar Juma’a Ana sa ran wasu ‘yan Najeriya 802 da suka makale a masarautar Saudiyya za su sauka a Abuja yau da gobe, Daily Trust ta ruwaito. An tsare su a wurare daban-daban da ake tsare mutane a Saudiyya kan batun kaura ba bisa ka’ida ba. Sakataren din-din-din na Ma’aikatar Harkokin Waje, Gabriel Aduda, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya ce za a karbi wadanda za su dawo din ne a Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja, ta hanyar jiragen sama biyu na Saudiyya.

‘Yan Nijeriya 802 da suka makale a Saudiyya za su dawo yau Hoto: IOM Nigeria Source: UGC “Za a kebe su a sansanin alhazai na FCT na tsawon kwanaki 14 daidai da ka’idojin da aka kafa na COVID-19. “Rukunin farko zai zo ne a ranar Alhamis, 28 ga watan Janairu da karfe 11:50 na safe, yayin da na biyu zai zo ranar Juma’a, 29 ga watan Janairu da karfe 10:35 na safe. “Wadanda za su dawo din za a karbi bakuncin dawowarsu ne daga jami’an ma’aikatar harkokin waje, da kwamitin shugaban kasa kan COVID-19 da sauran MDA da suka dace. “Bayan haka, ma’aikatar za ta sauƙaƙe hanyoyin zuwa garuruwansu na asali”

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings