X

‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi Sun Kammala Taro Kan Ka’idojin Aiki Da Dokar ‘Yancin Sarrafa Kudade

‘Yan majalisar dokokin jihar Bauchi sun kammala taron bita na yini biyu a jihar Kano kan sharruda da ka’idojin aiki da dokar ‘yancin kasashe kudade ga majalisun dokoki na jihohi a Najeriya wadda majalisar dokokin kasar tayi kusan shekara guda baya.

Sai dai shugaban majalisar dokokin ta jihar Bauchi Hon. Abubakar Sulaiman wanda kuma shine ke jagorantar kungiyar shugabannin majalisun dokoki ta jihohin Najeriya ya ce ya zuwa yanzu jihohi 10 ne kawai suka fara aiki da dokar daga cikin 36 na kasar.

Batun aiwatar da wannan doka shi ne babban kalubalen dake gaba bayan kwashe shekaru da dama ana gwagwarmaya, wadda ta rinka samun tirjiya daga bangaren gwamnoni, kuma daga bisani an samu nasara.

Hon. Abubakar Sulaiman shugaban kungiyar shugabannin majalisun dokoki na jihohin Najeriya kuma shugaban majalisar dokoki ta jihar Bauchi ya ce jihohi kamar Legas da Delta sun fara amma wasu suna jan kafa saboda matsalolin wajen aiwatarwa. Kuma suna sa ido akan harkokin.

Sai dai masana kimiyyar siyasa dake sharhi kan harkokin demokaradiyya na ganin akwai hakkin akan dukkanin majalisun jihohin su hanzarta samar da dokar kula da sarrafa kudaden su kuma gwamnoni su rattaba hannu akan dokar, kamar yadda Malam Kabiru Sa’idu Sufi ya ce.

To ko wane irin tasiri wannan ‘yancin samun kudade ga ‘yan majalisar dokoki zai yi ga makomar rayuwar al’uama?

Malam Kabiru Sa’idu Sufi wani masanin kimiyyar siyasa a Najeriya, ya ce ana ganin ce wa samun ‘yancin kai me game da abubuwa da dama musamman wadanda za su taimaka wajen yin dokoki masu inganci da suka shafi ‘yan kasa.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari:

Report din VOA

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings