X

Yan majalisa sun gayyaci Shugaban INEC kan zaben fid da gwani

Majalisar wakilai a Najeriya ta gayyaci shugaban hukumar zaben kasar da ya je gabanta ya yi bayani a kan kudin da za a kashe a kan zaben fid da gwani na ƴar tinke, wanda dama ke cikin sabuwar dokar zaben da ƴan majalisar suka zartar kwanan nan. 

Batun zaben fid da gwanin ya janyo ka-ce-na-ce a Najeriya, kasancewar gwamnonin jihohi suna adawa da tsarin ƴar tinken, yayin da ƴan majalisa ke cewa shi ne ya fi dacewa. 

Ƴan majalisar wakilan sun amince da aika wa shugaban hukumar zaben kasar, Farfesa Mahmud Yakubu goron gayyata ne, bayan dan majalisar daga jihar Kogi, Honorabul Leke Abejide ya gabatar da kudurin a jerin batutuwa masu bukatar kulawar gaggawa.

Ƴan majalisar sun ce suna jin ana cewa zaben fid da gwanin kadai idan jam’iyyun siyasar kasar za su yi shi kai-tsaye, to zai lashe fiye da naira biliyan 500.

A kan haka suka ce yana da kyau hukumar zabe ta fito ta fadi yadda maganar take, saboda ita ce a tsakiya kuma a karshe ita ce za ta yi aikin sa-ido a zaben fid da gwanin, da ma gudanar da zaben ma baki daya.

Daga karshe bakin ƴan majalisar ya zo daya, inda suka yanke shawarar gayyatar shugaban hukumar zaben domin ya je gaban kwamitin majalisar a kan kasafin kudi, da kuma kwamitin da ke kula da harkokin zabe domin jin yadda lamarin yake.

Kuma kamar yadda ƴan majalisar ke cewa sanin abin da ya kamata a yi a kan zaben fid da gwanin, musamman ta fuskar kudi zai yi fa’ida, a daidai wannan lokacin da suke gab da zartar da kasafin kudin sabuwar shekara.

Kazalika sanin girman dawainiyar da ke cikin zaben fid da gwanin na da muhimmanci sosai.

Batu ne da ke cikin abubuwan da ake kyautata zaton cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai yi la’akari da su, kafin ya yanke hukunci kan dokar zaben da ke gabansa.

Gwamnonin jihohi dai a nasu bangaren sun ce ba sa goyon bayan zaben fid da gwanin ta hanyar ƴar tinke, tun daga matakin gunduma zuwa sama saboda kudin da tsarin zai ci. 

A maimakon wannan tsari na zaben sun fi so a ci gaba da tsarin da ake amfani da shi wajen fitar da ‘yan takara, wato ta hanyar wakilai ko deliget (delegate).

To amma wasu na zargin cewa suna adawa da tsarin ne saboda zai karya lagonsu, ma’ana ba za su samu damar tankwara zabukan fid da gwanin ba. 

Tuni hukumar zaben Najeriyar kamar yadda rahotanni suka ambato wani jami`inta, ta tabbatar da cewa ta samu wasikar shugaban kasa da ke neman shawarwarinta a kan zaben fid da gwanin.

Bugu da kari jami’in ya ce hukumar za ta yi la’akari da abubuwan da za su kyautata demokuradiyya da ci gaban kasa, wajen bai wa Shugaba Muhammadu Buhari amsar wasikarsa.

DAGA JARIDAR BBC

Categories: Labarai
Tags: HAUSAlabarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings