Hukumomi a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya sun ce ma’aikata sun koma bakin aikin gyaran manyan turakun wutar lantarki, bayan da ‘yan Boko Haram reshen ISWAP suka tarwatsa manyan layukan wutar ranar Asabar.
Hare-haren Boko Haram dai sun yi wa turakun wutar lantarkin mummunar illa tsawon lokaci, abin da yasa birnin Maiduguri ke fama da rashin wutar lantarki tsawon watanni, amma hukumomin jihar sun ce sun dukufa wajen gyarasu. Ga karin bayanin da Zahraddeen Lawan ya aiko mana daga Abuja.
Hare-haren Boko Haram dai sun yi wa turakun wutar lantarkin mummunar illa tsawon lokaci, abin da yasa birnin Maiduguri ke fama da rashin wutar lantarki tsawon watanni, amma hukumomin jihar sun ce sun tukufa wajen gyara su.
Wani mutum da ya bukaci a boye sunansa ya shaida wa BBC cewa a ranar Asabar ne kungiyar Boko Haram reshen ISWAP suka dasa wa manyan turakun hudu bam al’amarin da ya yi sanadiyar tarwatsewarsu, a dai-dai kauyen Kuturu kusa da Auno cikin kaaramar hukumar Kondiga a jihar Borno.
Sai dai mutum ya ce ya ga ma’aikata suna kokarin gyarasu.
Hon Babakura Abbajato, Kwamishinan yada labarai na jihar Borno ta waya, ya tabbatar wa BBC cewa ana aikin gyaran manyan turakun wutar.
Ya ce ba su da wutar lantarki a Maiduguri fiye da wata shida, saboda haren-haren Boko Haram da suka yi sanadiyar tintsirewar turakun wutar har guda takwas a baya, inda ya ce suna kan aikin gyaransu ne, sai ga shi ‘yan ISWAP sun sake lalata wasu.
Haka kuma Hon Babakura ya ce kamfanin mai na NNPC zai samar da wata tashar wutar lantarki mai karfin mega watt 50 a cikin Maiduguri, nan da wani lokaci karin akan kokarin da suke yi na dawo da hasken wutar lanatarki a birnin Maiduguri da sauran sassan jihar.