Duk da artabun da aka yi tsakanin ‘yan-bindiga da wasu jami’an tsaron da su ka sami hadin kan ‘yan- sintiri a kudancin karamar hukumar Birnin Gwari a jahar Kaduna, ‘yan-bindigan su sake kai wani hari inda su ka kashe wasu manoma a yankin Ganin-Gari na karamar hukumar.
A yammacin Lahadin da ta gabata ne dai ‘yan-bindiga dauke da makamai akan babura su ka kai hari garin Ganin-Gari inda su ka kashe mutane biyu sannan su ka sace mutane da babura sai dai akan hanyar komawa mafakar su sai jami’an tsaro su ka yi musu kwanton Bauna inda su ka kashe wasu kuma su ka kubutar da mutanen da ‘yan-bindigan su ka sato, kamar dai yadda shugaban kungiyar cigaban masarautar Birnin Gwari, Malam Ishaq Usman Kasai ya shedawa Muryar Amurka.
Ya ce ‘yan-sandan da ke aiki a yankin da kuma wasu ‘yan-banga ne su ka sami labarin harin ‘yan-bindigan sai su ka tare hanyar da ‘yan-bindigan kan bi don komawa daji inda su ka yi nasarar kashe wasu sannan kuma wasu su ka ranta a na kare su ka bar mutane da babura da kuma dabbobin da su ka sato daga kauyen na Ganin-Gari.
Yankin Birnin Gwari dai na cikin yankunan da su ke fama da matsalolin tsaro na dogon lokaci abun da ya sa al’umar yankin ke nanata bukatar dauki daga gwamnati sai dai gwamnatin jahar Kaduna ta sha jaddada irin kokarin da take wajen magance matsalar tsaro kamar dai yadda gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasuru Ahmed El-rufa’i ya taba shedawa manema labaru.
A cewar gwamna El-rufa’i, na’urorin zamanin da gwamnatin jahar Kaduna ke karawa a wasu yankuna da kuma jirage marasa matuka za su taimaka wajen magance matsalar tsaro a jahar Kaduna.
Ganin yadda matsalar tsaro ta ta’azzara a yankunan karamar hukumar Birnin Gwari dai ya sa jagororin yankin irin su Malam Ishaq Usman Kasai bayyana cewa , zabi biyu kawai su ka rage yanzu wato gwamnati ta sauya salo don nuna ita gwamnati ce ko kuma ta bar mutane su dauki makamai idan ita ba za ta iya ba.
A baya dai hare-haren ‘yan-bindiga a yankin Birnin Gwari sun fi yawa akan hanyar zuwa Kaduna sai dai yanzu ‘yan-bindigan sun koma afkawa garuruwan yankin abun da ke kara adadin mutanen da ke kaura zuwa yankunan da ke da saukin matsalolin tsaro.