Wasu ‘yan bindiga kimanin mutum 40 ne suka kai hari a kauyen Kawu da ke karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja da sanyin safiyar Alhamis inda suka yi awon gaba da mutane 23.
Kawu yana da iyaka da jahohi biyu: Neja da Kaduna.
Kansilan yankin Abdulmumini Zakari wanda shi ne mataimakin kakakin majalisar a majalisar ya ce ‘yan bindigar sun isa yankin ne a ranar Laraba daga dajin Kuyeri da ke jihar Kaduna.
Ya bayyana cewa, “Sun raba kan su gida-gida, wasu kuma suka shiga fadar hakimin gundumar, Alhaji Abdurrahman Danjuma Ali, inda suka yi awon gaba da dansa Lukman da matarsa, wanda ya aura makonni biyu da suka wuce. Wasu kuma sun kai hari gidan Alhaji Alhassan Sidi Kawu, Marafa na Kawu kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP na unguwar Kawu. Sun yi awon gaba da shi tare da ‘ya’yansa hudu.”
‘Yan bindigan sun kuma shiga harabar Sarkin Pawan Kawu, Gambo S Pawa, inda suka yi awon gaba da shi tare da matansa biyu da wasu ‘ya’yansa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, S.P Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin a martanin da ta mayarwa wakilinmu a jiya.
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai farmaki kauyen Kawu da ke kan iyaka da karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna, inda suka yi garkuwa da mutane. Maganar gaskiya ’yan bata-gari sun kai farmaki a wannan yanki na gaba daya inda suka tsere zuwa cikin jihar Kaduna,” inji ta.