Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki jihar Imo a ranar Asabar din da ta gabata, inda suka kashe wani magidanci mai ‘ya’ya hudu a wani bikin binne shi a garin Atta da ke karamar hukumar Ikeduru ta jihar. An ce an harbe wanda aka kashe a gaban matarsa da ‘ya’yansa.
Wakilinmu ya tattaro cewa wadanda suka kashe shi sun gudu daga wurin bayan sun yi harbin, lamarin da ya sa masu zaman makoki suka firgita. Shedun gani da ido sun ce ‘yan sanda karkashin jagorancin jami’in ‘yan sanda reshen Imo, sun isa wurin jim kadan da faruwar lamarin. Har ila yau, an ce wasu ‘yan bindiga sun harbe wani matashi da ba a san ko su waye ba a Amaraku da ke karamar hukumar Isiala Mbano a jihar. Dukkanin al’amura biyu sun faru ne kasa da sa’o’i 24 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wani jami’in hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC). Jami’in mai suna Engr. Kingsley Okorafor, an ce an sace shi ne da sanyin safiyar Juma’a a gidansa da ke Umulogho a karamar hukumar Obowo ta jihar. Majiyoyi sun ce wadanda suka yi garkuwa da shi sun tuntubi iyalansa inda suka bukaci a biya fansar Naira miliyan 10. Wani mutum mai suna Collins, ya shaida wa wakilinmu cewa matashin da aka kashe a Amaraku dan uwansa ne. Ya ce, “Ina cikin kaduwa. Wasu ‘yan bindiga/ masu garkuwa da mutane da ba a san ko su wanene ba ne suka kashe dan uwana a unguwar Amaraku jiya da yamma. Har yanzu ina cikin kaduwa.” Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar, CSP Mike Abattam, ya kasa samun jin ta bakinsa.