Rahotanni daga jihar Katsina a arewacin Najeriya na cewa ƴan bindiga sun kashe wani kwamshina a jihar Katsina a arewacin Najeriya.
Kwamishinan ƴan sanda na jihar ya tabbatar da lamarin a wani taron manema labarai a ranar Alhamis. Wasu rahotanni sun ce lamarin ya faru ne ranar Laraba da daddare.
Sannan wasu rahotannin daga jihar Neja a arewa ta tsakiyar ƙasar kuma ƴan bindigar sun kashe mutum 16 a masallaci wasu goammai kuma sun jikkata a wani hari da ‘aka kai ƙauyen Ba’are a karamar hukumar Mashegu da ke jihar Nejan.
Ahmed Ibrahim Matane shi ne sakataren gwamnatin jihar ta Neja, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na safiyar ranar Laraba.
Kwamishinan ƴan sanda ya ce tuni an fara bincike kan mutuwar kwamishinan kmiyya da fasaha na jihar Katsinan, “don haka babu wani dogon bayani da zan iya yi yanzu, sai dai a saurara sai binciken ya yi nisa,” in ji shi.
Ya ce tuni aka kai gawar mamacin asibiti.
Bayanai sun ce an kashe Kwamishina Dr Rabe Nasir ne a gidansa da ke rukunin gidaje na Fatima Shema Estate a cikin birnin Katsina.