Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashin daji ne sun kashe jami’in ɗan sanda (DPO) yayin wani hari a garin Jibiya na Jihar Katsina ranar Talata da dare.
DSP A. A. Rano wanda shi ne DPO na Jibiya, ya rasa ransa ne lokacin da ‘yan fashin suka afka wa garin suna harbe-harbe kan mai tsautsayi don firgita mazauna yankin.
Sannan maharan sun kuma harbi wani soja a ƙafa kuma daga baya ya rasu, kazalika sun harbi wani kwamanda na soji da yanzu haka yana asibiti a kwance.
Jaridar BBC ta wallafa cewa ta tabbatar da labarin daga sahihan majiyoyi da dama, bayan da suka kira mai magana da yawun ƴan sandan jihar Katsinan Gambo Isa amma bai ɗauki waya ba.
Amma an ga wani saƙo da SP Gambo Isa ya wallafa na ta’aziyyar marigayin a wani zaure na WhatsApp, sannan majiyoyi daga Jibiyan sun tabbatar SP Gambo Isa ya je wurin da abin ya faru.
Wani mazaunin yankin ya faɗa wa BBC din Hausa cewa lamarin ya faru a kan idonsa, yayin da tawagar haɗin gwiwar jami’an tsaro ta ‘yan sanda da sojoji suka fafata da ‘yan bindigar kafin daga bisani su gudu cikin daji da mutanen da suka yi garkuwa da su.
Maharan sun sace wata mata da diyarta wanda a garin ceto su ne aka harbe DPO ɗin.
A ranar Litinin da dare ma wasu ‘yan fashi sun kashe mutum 12 tare da kama wasu da ƙona gidajen garin Guga na Ƙaramar Hukumar Bakori ta Katsina.