Jama’a da dama a shafukan sada zumunta musamman ƴan arewacin Najeriya sun fusata sakamakon wani bidiyo da ake ta yadawa da ke nuna yadda aka kashe wata mata da yara a Jihar Anambra da ke kudancin Najeriya.
Wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar IPOB ne suka kashe matar mai suna Harira Jibril, mai shekara 32, da ƴaƴanta Fatima, mai shekara tara, da Khadijah, mai shekara bakwai, da Hadiza, mai shekara biyar, da Zaituna, ‘yar shekara biyu da wasu aƙalla mutum shida a jihar.
Ƴan sandan Najeriya sun tabbatar da kisan inda suka ce suna neman waɗanda suka aiwatar da wannan aika-aika.
jaridar BBC wallafa cewa ta tattauna da mijin matar mai suna Jibril Ahmed wanda a cewarsa matar tasa wadda ke ɗauke da cikin wata tara na hanyar dawowa daga ziyarar da ta kai tare da yaransu Orumba North wanda a hanyar ne aka tare su aka kashe su.
Alhaji Usman Abdullahi wanda shi ne Sarkin Hausawan Ihiala a Anambra shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce matar asalin ƴar Jihar Adamawa ce daga arewacin Najeriya.
Sarkin Hausawan wanda yanzu haka yake gudun hijira ya ce al’ummar Hausawa na cikin wani hali a Jihar Anambra.
Sarkin Hausawan ya koka kan kashe-kashen inda ya ce ‘yan arewa da ke zama a jihar sun yanke shawarar za su dawo gida arewa.
A cewarsa, a Ƙaramar Hukumar Ihiala wanda a nan yake, babu wani Bahaushe da ya rage sakamakon duk sun yi gudun hijira saboda barazanar ƴan Ƙungiyar ta IPOB.
Ko a kwanakin baya sai da wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar IPOB ne suka kashe wasu sojoji biyu da suke shirin yin aure a Jihar Imo.